Kamfanoni arba’in da daya na kasa da kasa sun yi alkawarin samar da ayyukan yi, da horar da ‘yan gudun hijira 250,000 a Turai. Amma ta yaya 'yan gudun hijira a Afirka za su amfana da irin wannan kokari? Dr. Manasseh, shugaban kungiyar agajin jin kai ta Impact-Trust International ya mana karin haske.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 89.3 ne aka tilastawa barin gidajensu a fadin duniya. Daga cikinsu akwai kusan 'yan gudun hijira miliyan 27.1, kuma kusan kashi 41 cikin 100 daga cikinsu, ba su kai shekaru 18 ba.
A Jamhuriyyar Nijar sannu a hankali matasan wasu biranen kasar musamman ma na birnin Yamai, sun fara farfado da wasu al'adun gargajiyar kasar da aka fara mantawa da su musamman ma a bikin aure.
Yajin aikin da masu dafa abinci a makarantu ke yi na iya tilasta wa yaran makaranta da ke cin gajiyar shirin ciyar da dalibai da gwamnatin Ghana ta bullo da shi zama da yunwa.
Masu sharhi sun ce ana fargabar cewa karuwar rikicin Sudan a yankin Darfur na iya yaduwa zuwa kasashe makwabta.
A jawabin da ya yi wa ‘yan kasar a bikin ranar dimokuradiyya, Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da sadaukar da kai domin ci gaban kasar.
Muryar Amurka ta tattauna da Nastura Ashir Shariff, wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullun a game da wasu daga cikin abubuwan da shugaba Tinubu ya tabo a jawabin na shi na ranar dimokradiya.
Tun bayan dawowar mulkin dimukradiya a Najeriyar a 1999, a jihar Kano wacce ta fi kowacce yawan mutane a arewacin Najeriya, kuma cibiyar kasuwancin yankin, an samu cigaba da kuma akasin haka, sakamakon rashin dorewar manufofin gwamnati.
Biyo bayan sanarwar cire tallafin mai da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi, mun duba tasirin sanarwar cire tallafin man kan halayen 'yan kasuwa da sauran al' ummar Jos a Arewa ta tsakiyar kasar.
Tun bayan ayyana cire tallafin man fetur kawunan ‘yan Najeriya ya rarrabu, yayin da wasu ke goyon baya, wasu na sukar matakin, saboda su na ganin zai shafi da dama daga cikin marasa galihu da ke fama da matsin tattalin arziki.
Yemi Mobolade 'dan asalin Najeriya wanda ya zo nan Amurka karatu shekaru 27 da suka gabata, ya kafa tarihi ba kawai na zama bakar fata na farko ba, har ma da zama Magajin Garin na farko wanda ba 'dan jam’iyyar Republican ba a cikin shekaru 45 a Colorado Springs.
Mutane a Ghana su na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a game da sabon bashin da gwamnatin kasar ta ciwo daga IMF na dala biliyan 3 a makon jiya.
Domin Kari