A zaben shugaban kasar Amurka, ba wai samun mafi yawan kuri’u ke da muhimmanci ba, a’a, muhimmin abu shi ne lashe mafi yawan kuri’un gundumomin zabe wato Electoral College, da ko wace jiha take da gwargwadon adadin nata. Ga yadda tsarin yake.
Har yanzu muna kam batun kiwon lafiyar. Jami’ai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce suna kara azama wajen shawo kan barkewar cutar kwalara, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a baya-bayan nan da ta raba kusan mutane miliyan biyu da muhallansu.
A duk bayan shekara hudu, fafutukar lashe zaben shugaban kasar Amurka ta na fin raja’a ne a muhimman jihohin raba-gardama.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 1.9, wato kashi 86% na mutanen Gaza sun rasa matsugunansu, kuma da yawa suna zaune ne a sansanonin 'yan gudun hijira, inda suke fama da karancin abinci da karancin sha’anin kula da lafiya.
Shekara guda kenan da barkewar rikici a Gaza sakamakon harin da kungiyar Hamas ta kai kan Isra'ila wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 1,200, rikicin da ya rikide zuwa yaki, kuma ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 40,000 tare da barazanar rikicin zai mamaye yankin gabas ta tsakiya.
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
Domin Kari