Wasu matasa 50 masu kirkira kuma shugabanni daga kasashen Afirka 19 sun hallarci wani shiri na tsawon makonni 3 inda zasu samu horo kan shugabanci da kuma fannin bunkasa kwarewar su a babban birnin kasar Ghana, Accra ta hanyar shirin Young African Leaders Initiative ko kuma YALI a takaice.
Shugaban Amurka Joe Biden, a ranar Talata, ya ayyana kokarin gwamnatinsa na ganin an dakile sai da fentanyl da sinadaren da ake amfani da su wajen sarrafa mummunar kwayar bayan wata yarjejeniyar da aka kula da shugabannin China da Mexico a kwanan nan.
Batula Ali tayi fintikau inda ta kasance mace ta farko dake aikin tuka motar daukar marasa lafiya a sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma na tuka dake Kenya.
Babban Darekta Janar mai kula hukumar da dakile yaduwar cutar ta AIDS NACA Gambo Aliyu, yayi bayani a game da ci gaban da hukumar ta samu a yakin ta da cutar SIDA a Najeriya da ma kalubalolin da ake fuskanta na kyamatar masu cutar.
Cibiyar binciken al’amuran noma wato Institute of Agricultural Research ta jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ta samar da wani nau’in masarar da kwari basa ci mai suna TELA MAIZE. Ana fatar irin masarar zai taimaka wajen magance matsalar karancin girbi sakamakon kwari dake far ma gonaki.
Yayin da ake samun karuwar matsalar lalata da cin zarafi a Maiduguri, har ma a sansannonin ‘yan gudun hijira wasu kungiyoyin fafutukar mata suna bayyana damuwar su.
A Ghana, wani sabon kamfani ya samarwa gidaje da makarantu sauki bayan da ya kafa masu na’urar wutar lantarki mai amfani da hasken rana.
Domin Kari