Farashin raguna kan kama ne daga N160,000 zuwa N170,000, wadanda kuma ake shigo da su daga sauran kasashe makwabta Najeriya kuma, sukan kai kimanin N600,000 zuwa N700,000.
Wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar ta kai ziyara kasuwar Apo da ta Wuse a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ta tattauna da wasu 'yan kasuwa.
A ranar 13 ga watan Yuli shirin karin kudin tikitin da aka yi zai fara aiki a daukacin jihar.
A cigaba da yunkurin nemo masalaha ga yawan rigingimu da ake samu tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya, gwamnatin tarrayar kasar karkashin ma’aikatar noma da raya karkara ta kaddamar da wani sabon shiri da zai mai da hankali kan harkokin kiwo da inganta noma.
Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya kai ziyara kasuwar Monday Market da ke cikin birnin Ilori a jihar Kwara.
Farashin man fetur ya haifar da kaso mafi girma na hauhawar farashin kayayyakin masarufi, hayar gidaje, farashin tikitin hawa jiragen sama da sauran abubuwa da dama.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bukaci kungiyar Tarayyar Turai da ta kara himma wajen taimaka wa kasashe masu tasowa don jure barnar da annobar cutar coronavirus tayi.
Kididdiga ta nuna cewa a duk shekara kusan tan miliyan 7 na shinkafa ake ci a Najeriya.
Abdullahi Mansoor, manomi ne kuma mazaunin Yankin Adamawa, ya yi farin ciki da wannan labari, ko da yake yana taka-tsantsan da irin wannan alkawari na gwamnati.
Shirin Kasuwa na wannan makon ya kai ziyara kasuwar Garki Village da ke Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.
Bayan watanni biyu da gwamnatin Ghana ta sanar da bude iyakokinta, hukumomi a Togo sun sanar da bude nasu iyaka da Ghana domin karfafa kasuwanci da yaki da ta'addanci.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.