Wata mummunar gobarar da ta auku a kasuwar Karu da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa ta yi sanadin janyo asarar dukiya mai yawa.
Da safiyar Laraban nan ne aka wayi gari da samun tashin gobara a matatar man fetur ta Dangote a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Marasa rinjayi a Majalisar dokokin Ghana sun bayyana damuwarsu kan kalubalen da darajar kudin Ghana wato Sidi ke fuskanta da har yanzu aka gaza samar da mafita, suna masu gargadin cewa lamarin zai kara ta’azzara.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Olayemi Cardoso ya ce kayayyakin abincin da gwamnati take saya don rabawa mabukata na daga cikin dalilan da suke kara hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Najeriya ta samu jarin dalar Amurka miliyan 600 na samar da kayayyakin aiki a tashar jiragen ruwa daga kamfanin jigilar kayayyaki na kasar Denmark A.P. Moller-Maersk MAERSKb.CO, kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar ranar Lahadi.
A makon da ya gabata dan takarar Shugaban kasa a zaben 2023 karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya yi kira da a gudanar da binciken “gaggawa” kan zargin na Ningi.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote na shirin kafa wata kungiyar hada-hadar man fetur, mai yiwuwa a birnin Landan.
'Yan kasuwar canjin kudi da dama sun nuna rashin gamsuwa da soke lasisin sama da kamfanonin canji 4000 da babban bankin Najeriya CBN ya yi.
Babban Bankin Najeriya CBN ya soke lasisin wasu kamfanonin canjin kudi 4,173, cikin kimanin 5000 da ake da su.
A cewar masanin, lokaci ya yi da matasa za su kara mayar da hankalinsu kan koyon ilimin na'ura mai kwakwalwa wanda hakan zai ba su dama su yi aiki daga ko'ina a duniya.
Farashin hannun jari Access Holdings na Najeriya ya fadi da kaso 6.26 a yau yayin da masu hannun jari a kamfanin ke alhinin rasuwar Herbert Wigwe.
Kamfanin na Dangote ya kara da cewa har ya turawa EFCC wasu bayanai a mataki na farko, amma jami’an hukumar suka ki karbar bayanan suka kuma matsa cewa sai sun kai ziyara hedkwatar kamfanin.
Domin Kari
No media source currently available