Hukumar kwastam ta ce a fili ta ke gudanar da gwanjan kaya kuma kowa zai iya shiga yanar gizo ya ga yanda a ke gudanar da cinikin.
Gidajen gyara hali a Najeriya, na ci gaba da kasancewa matattarar masu aikata laifuka mabambanta inda wasu masu laifi kan iya koyon wasu laifuka na daban musamman wadanda ba su da aikin yi kafin a kai su kurkuku.
Watanni shida da cikar wa'adin mulkin shugaba Mohammadu Buhari, bincike ya nuna cewa jimlar basussuka da gwamnatin Tarayya ta ciwo da sauran lamuni da ta yi sun kai Naira triliyan 71.5 amma masana tattalin arziki sun bayyana ra'ayi mabanbanta akan haka.
Rahotanni sun ce filayen Kalmoni da za a kaddamar da aikin, na dauke da arzikin man da yawansa ya haura sama da ganga biliyan daya.
Shugaban na Najeriya ya yi la’akkari da yadda wannan matsala ta samun kudaden ketare a farashi daban-daban take haifar da cikas ga tattalin arzikin kasa.
Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, masu sayan amfanin gona a kakar bana, na bin manona har gonakinsu suna cinikayyar kayan abinci da manoman suka samar, inda suke biyan duk abin da suka saya kudi a hannu
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana sa ido a kan abubuwa dake faruwa a game da sauyin mallakar katamfaren kamfanin sadarwar zamani, Twitter, biyo bayan sayen kamfanin da sabon shugabansa Elon Musk ya yi.
Wani babban al’amari da har ila yau ya sa kudaden da kamfanin yake kashewa ya karu shi ne, shirin nan na Metaverse da ya tsunduma kansa a ciki, wanda yake cin makudan kudade.
Gabanin nan, mataimakin Ministan ya bayyana yanayin da Nijar take ciki a yau, inda ya ce, a shirye kasar take ta amshi masu zuba hannun jari.
Kasuwar Lafiya-Lamurde da ke karamar hukamar Lamurde a jihar Adamawa kasuwa ce da ke chi mako-mako kuma ita ce kasuwar kayan abinchi da ake alfahari da ita a jihar da ma makwabtanta.
Sama da tan miliyan tara na shinkafa ne ake shigowa da shi a yankin yammacin Afirka, wanda ke lakume kusan dala biliyan 3.4 a cikin lissafin kudin shigowa da kaya a shekarar 2021.
Domin Kari
No media source currently available