Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga tsohon mataimakinsa dan takarar shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar.
Da yawan ‘yan kasar Sudan suna kokawa game da yadda gwamnatin Sudan din ta sake rage darajar kudin kasarta ranar Lahadi, da kusan rabi, yayin da tattalin arzikin kasar ke cikin halin kaka-ni-kayi.
Hukumar zaben Najeriya tace har yanzu kofa tana bude na shigar da sunayen 'yan takara,a kamar yadda aka yayata tun farko ba.
Da alamu wata sabuwar rigima ce ke kokarin kunno kai a tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Borno, sakamakon zaben fidda gwani da aka yi a makon jiya.
A karon farko gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, ya maida martani game da zaben tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP da cewa basa tsoron karo da maza.
Kamar yadda akasarin masu hasashe su ka hango tun da farko, yanzu ta bayyana cewa za a buga ne tsakanin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, a zaben da akasarin masu lura da al'amura ke ganin za a yi ta - a kalla - a siyasance.
Da alama jam’iyyar APC mai mulkin jihar Zamfara, ba ta da ‘yan takara a zaben shekara ta 2019 mai zuwa, a dai dai lokacin da wa’adin da hukumar zaben Najeriya ta baiwa jam’iyyu domin gabatar da ‘yan takara ya kure wa jam’iyyar ta APC a jihar.
A dai-dai lokacin da shugaba Buhari ke neman hadin kan ‘yan APC don zarcewa kan mulki a 2019, har yanzu a jihohi da dama a na samun korafin rashin adalci daga zaben fidda gwani na jam’iyyar musamman kan kujerar gwamna.
Bayan kammala zaben fidda 'yan takara a Jihar Adamawa, an ayyana gwamnan Jihar a matsayin wanda ya lashe zaben.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gwamnoni guda takwas karkashin jagorancin gwamnan Zamfara, domin neman hanyar warware matsalolin da suka shafi zabukan fitar da ‘yan takara a jam’iyyar APC.
Domin Kari