Rahotanni sun ce bayan da Atiku ya rattaba hannu a yarjejeniyar, ya yabawa shugaba Buhari saboda sanya hannu da ya yi a yarjejeniyar. Amma ya kalubalance shi da ya sa hannu a kudurin dokar zaben da aka yi wa garanbawul wacce majalisar dokokin kasar ta gabatar masa.
yanzu haka ana ci gaba da cece kuce da kuma maida martani kan karar da hukumar EFCC ta kai wasu manya 'yan siyasa a jahar Taraba saboda badakalar Naira Miliyan 450 da su ka karba a zaben 2015, ciki har da dan takarar gwamanan APC a shekara mai zuwa.
An kara jan hankalin talakawa wajen zaben shuwagabanni a zaben game gari mai zuwa a Najeriya.
“An ce mana mu jam’iyar PDP ba mu da magoya baya a arewa maso yamma, wadannan ba jama’a ba ne.? In ji Atiku.
“Ina mai tabbatar muku cewa, ni ne (Buhari) na asali, a kwanan nan ma zan yi bikin cika shekaru 76 da haihuwa kuma zan ci gaba da kasancewa da karfina.”
Wasu matasa daga jihohin Pilato da Kogi sun bayyana kudirinsu na bijirewa shiga bangar siyasa da haddasa fitina a kasa.
Shugaban Jam'iyar PDP na Kasa yayi kira da shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmoud Yakub da na 'Yan sanda Ibrahim Idris, su yi sauka daga kan mukaman su, saboda zargin da yake musu na cewa baza su yi musu adalci ba a zaben 2019.
Shugaba Buhari har ila yau, ya yi kira ga wadanda ba su samu nasara a zaben fidda gwani a jam'iyyunsu ba, da su fifita zaman lafiyar kasarsu sama da bukatunsu na kansu.
Yayin da jam’iyyu ke kammala fidda 'yan takara domin fuskantar zabukan dake tafe a Najeriya, yanzu haka Matasa da kuma mata sun yunkuro domin damawa da su a zabe, musamman ta wajen tsayawa takara.
Kudurin wata sabuwar doka da Majalisar Dokokin Najeriya ta rattabawa hannu za ta kyautata jin dadin Nakasassu a daukacin kasar.
Kasashen na Amurka da Birtaniya da kuma kungiyar ta tarayyar turai sun ce za su sa ido su ga yadda wannan zangon gangamin yakin neman zabe zai kasance.
Daga Yau Lahadi ne hukumar zaben Najeriya ta amince 'yan takar shugabancin Najeriya da 'yan takarar kujerun majalisar dattawa da ta wakilai su fara yakin neman zaben da za a yi a watan Fabrairun 2019.
Domin Kari