Majalisar Dattawan Najeriya tareda hadin gwiwa da ta Wakilai sun amince da dokar da za ta hana a kyamaci nakasassu har a kaiga yi masu wariya, musamman abubuwan da suka shafi aiyukansu na yau da kullun.
Mataimakin Shugaban Kwamitin kula da harkokin Nakasassu a Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Garba Marafa ya ce dokar za ta kunshi komi da komi da ya shafi nakasassu, kamar yin gini da matakalar nakasassu da wurin ajiyar motoci.
Shi ma dan Majalisar Dattawa Yusuf Abubakar Yusuf, ya kara da cewa nakasassu masu ilimi dokar ta bada damar a dauke su aiki, kuma a biya su daidai da sauran ma'aikata da ba su da Nakasa.
Amma daya daga cikin Nakasassu masu larurar makanta, Ali Yahaya Gwarzo ya ce sai lokacin zabe ya zo ne ake tada maganar kyautata wa Nakasassu saboda haka, a ganinsa ba giringirin ba dai, ta yi mai.
Facebook Forum