Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a Abuja tare da wasu tare da wasu kusoshin jam’iyarsa ta APC mai mulkin kasar, inda shugaban kasar ya ya gargadi yan majalisar da suyi kampe a kan ‘ka’ida da manufa mai kyau ba tare da ‘batanci ko cin zarafin kowa ba.
Dan takarar shugaban kasa karkashin tututar Jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yace babu adalci a yadda aka raba mukamai a gwamnatin Buhari.
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna gazarwar gwamnati mai ci kan matakan da take dauka wajen tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, da kuma yadda shi zai tunkari matsalar Boko Haram idan aka zabe shi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kare matakan da gwamnatinsa ke dauka wajen magance matsalar tsaro da ta addabi kasar, ku kalli wannan kashi na farko na hirar da Aliyu Mustapha Sokoto ya yi da shi domin bayyana ra’ayinku.
Shugaba mai ci Janar Muhammadu Buhari na jam’iyar APC, da kuma dan takarar babban jam’iyar hamayya PDP tsohon mataimakin Najeriya Alha Atiku Abubakar Wazirin Adamawa sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan harkokin tsaro.
Kadan daga cikin abubuwan da za kuji ke nan a wata tattaunawa ta musamman da dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, a shirin mu na safe idan Allah ya kai rai ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2019.
Kadan daga cikin abubuwan da za kuji ke nan a wata tattaunawa ta musamman da shugaba Muhammadu Buhari, a shirin mu na safe idan Allah ya kai rai ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2019.
Sai dai a cewar Rafsanjani, “babbar nasarar da aka samu kan batun yaki da cin hanci da rashawar ita ce, ana ta maganar batun cin hanci da rashawa, saboda haka, wajen wayarwa da mutane kai, an samu nasara” a wannan fannin.
Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi tattaki har zuwa Najeriya inda Aliyu Mustapha Sokoto ya yi hira da shugaba mai ci Muhammadu Buhari da dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar kan zaben 2019 da ke tafe.
Majalisar limaman Abuja ta bukaci limamai su ci gaba da tsayawa kan gaskiya da gujewa marawa wani bangaren siyasa baya musammanma ganin gabatowar zaben shekarar 2019 dake tafe.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo, ya yi kira da shugabannin addinai da su yi wa kasar addu'a domin a yi zaben shekarar 2019 cikin lumana.
Kamar yadda al'adar ta ke, an tafka zafaffiyar muhawara tsakanin 'yan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam'iyyar APC mai mulki da PDP mai adawa.
Domin Kari