Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ake kira INEC a takaice, ta ja kunnen ‘yan siyasa da su kauracewa duk wata dabi’a ta rashin da’a lokacin gudanar da zabe.
A daidai lokacin da ake haramar zabe a Najeriya,yanzu haka wata sabuwa ta kunno inda kungiyoyin addini suka fara bayyana wadanda zasu goyawa baya a cikin yan takarar shugaban kasa,batun da ya soma jawo cece-kuce inda wasu ke ganin haka bai dace ba.
Biyo bayan sauya sheka da wasu manyan ‘yan PDP ciki har da tsoffin shugabannin jam’iyyar na kasa da na arewa zuwa APC mai mulki, PDP ta ce hakan rabuwa da rakai ne kuma mutanen ba su da wani tasiri
Yanzu babu sauran tababa game da dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC, jiya shugaba Buhari ya daga hannun gwamna mai ci, yayin kamfe da ya yi a jihar, inda ya karbi wasu jiga jigai daga ja'iyyun adawa cikin su harda tsoffin gwamnoni biyu.
An fara ca-car baki a tsakanin 'yan siyasa a Najeriya, gabanin zaben 2019.
Uwargidan mataimakin shugaban Najeriya, Dolakpo Osinbajo ta gargadi al’ummar Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatansu don gudanar da zabe a zabubbukan da za’a gudanar a kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa da Musulmi da Kirista sun san da cewar babu inda addinin Islama yace a kashe wani, kuma ayi kabbara. Ya kuma yi karin haske akan matakan da gwamnatinsa ke dauka na ganin an inganta tsaro a kasar.
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna gazarwar gwamnati mai ci kan matakan da take dauka wajen tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, musamman yadda satar jama'a don neman kudin fansa yayi yawa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce bai kamata talakawa su sake zaben gwamnonin da basu yi masu aiki ba, da ya hada da gaza biyan albashin ma’aikata.
Yayin da jam'iyyu da 'yan sisaya a Najeriya ke ci gaba da yakin neman zabe domin tunkarar babban zaben kasar da za'ayi a watan gobe, Jam'iyyar hamayya ta PDP a jihohin Jigawa da Neja tace ta daura damarar dawo da gwamnati a wadanndan jihohi.
Domin Kari