Ku ci gaba da bibiyan shirye-shiryenmu na rediyo domin sauraren sabbin tambayoyi da sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a da muka yi.
A yau Juma'a dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya kai ziyara Muryar Amurka inda ya mayar da martani kan kalaman da gwamnatin Najeriya ta yi dangane da zuwansa Amurka.
Dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyar hamayya a Najeriya PDP, Alh Atiku Abubakar yana ziyara a Amurka inda ya gana da wadansu ‘yan majalisar dokokin kasa, yayinda a yau yake shirin zuwa ma’aikatar harkokin wajen Amurka
Kamfanin sada zumunta na Facebook yace zai fadada damammaki ga 'yan siyasa su tallata manufofi da tsare-tsaren su, yayin da a hannu guda kuma kamfanin ke daukar tsauraran matakan dakile yunkurin yin amfani da kafar sa wajen yada kalaman batanci a tsakanin 'yan siyasa.
Yayin da babban zabe a Najeriya ke ci gaba da karatowa, gwamnatin Amurka ta bayyana damuwa game da ayyukan Jami'an tsaron kasar a lokacin gudanar da zaben.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ake kira INEC a takaice, ta ja kunnen ‘yan siyasa da su kauracewa duk wata dabi’a ta rashin da’a lokacin gudanar da zabe.
A daidai lokacin da ake haramar zabe a Najeriya,yanzu haka wata sabuwa ta kunno inda kungiyoyin addini suka fara bayyana wadanda zasu goyawa baya a cikin yan takarar shugaban kasa,batun da ya soma jawo cece-kuce inda wasu ke ganin haka bai dace ba.
Biyo bayan sauya sheka da wasu manyan ‘yan PDP ciki har da tsoffin shugabannin jam’iyyar na kasa da na arewa zuwa APC mai mulki, PDP ta ce hakan rabuwa da rakai ne kuma mutanen ba su da wani tasiri
Domin Kari