An dai yi ta yamadidin cewa jifan ta aka yi, amma jarumar ta bayyana akasin hakan.
Fitaccen mawakin Najeriya, Olanrewaju Abdul-Ganiu Fasasi wanda aka fi sani da Sound Sultan, ya rasu.
A ‘yan watannin baya, Maryam Booth ta wallafa a shafinta na Instagram cewa a taya mahafiyarta da addu’a saboda za a yi mata aiki.
“Da wannan babban kifi yana cikin korama amma yanzu wannan babban kifi ya shigo cikin teku.” Ganduje ya ce a lokacin da Zango ya kai masa ziyara.
Naja’atu ta fara fitowa a finan-finan Kannywood tun tana ‘yar matashiya inda daga baya ta zama daya daga cikin fitattun jarumai mata.
A kwanan mabiyan jarumar a shafin Instagram suka kai miliyan daya, yayin da ba kasafai ake samun jarumai mata masu shekarunta da irin wannan adadi ba.
“Kowa ya bar gida, gida ya bar shi.” Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram dauke da hotuna da wani bidiyo da ya nuna shi tare da Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Wani matashi mai shekaru 23 da haihuwa, ya yi wuf da wata sananniyar ‘yar siyasa mai shekaru 45 a jihar Adamawa.
Ba dai kasafai ake samun wakokin Hausa suna samun masu kallo kamar haka a shafin YouTube cikin dan kankanin lokaci ba kamar yadda bincike ya nuna.
Ummi ta kuma nuna takaicinta kan yadda mutane da dama suka yi ta "zaginta" a lokacin da al’amarin ya faru, tana mai cewa kamata ya yi, a yi mata nasiha ba a ci mata mutunci ba.
Sai dai sanarwar da darekta Aminu Saira ya fitar, ba ta ambaci kafa ko tashar da za a haska fim din na Labarina ba.
Zhao ta lashe kyautar lanbar yabo na Oscar a matsayin babban darakta na "Nomadland," ta kuma zama mace ta biyu kuma mace ta farko da ba farar fata ba da ta lashe kyautar.
Domin Kari
No media source currently available
Ya Fitattun Mutane Ke Amfani Da Kafofin Sadarwa?