Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zango Ya Sake Komawa APC


Adam A. Zango (hagu) da gwamnan Kogi, Yahaya Bello (dama) (Instagram/ Adam Zango)
Adam A. Zango (hagu) da gwamnan Kogi, Yahaya Bello (dama) (Instagram/ Adam Zango)

“Kowa ya bar gida, gida ya bar shi.” Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram dauke da hotuna da wani bidiyo da ya nuna shi tare da Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya koma bangaren jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriya.

Jarumin na Kannywood da ke arewacin Najeriya, ya wallafa komen da ya yi ne a shafinsa na Instagram a ranar Talata inda aka gan shi tare da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

“Kowa ya bar gida, gida ya bar shi.” Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram dauke da hotuna da wani bidiyo da ya nuna shi tare da Gwamna Bello.

“Ga Adamu Zango a nan, muna maka barka da zuwa, ga shi sun dawo gida.” Gwamna Bello ya ce a cikin bidiyon mai tsawon dakika 29.

Gabanin zaben 2019, Zango ya sauya sheka ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, inda har ya gana da dan takarar shugaban kasar jam'iyyar Atiku Abubakar, ya kuma nuna magoya bayansa su zabe shi.

Adam A. Zango a lokacin da ya daga hannun Atiku Abubakar (Hoto: shafin Instagram na Zango)
Adam A. Zango a lokacin da ya daga hannun Atiku Abubakar (Hoto: shafin Instagram na Zango)

“An ba ni mukamin jakadan jam’iyyar PDP.” Zango ya rubuta a shafinsa na Instagram a watan Fabrairun 2019, a lokacin da ya koma PDP.

Zango koma PDP a wancan lokacin, ‘yan watanni bayan da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, ta hada wani bikin karrama jaruman dandalin shirya fina-finan Kannywood a shekarar 2018.

Aisha Buhari, (dama) da Adam A Zango, (hagu) a shekarar 2018 (Hoto: Instagram, aishambuhari)
Aisha Buhari, (dama) da Adam A Zango, (hagu) a shekarar 2018 (Hoto: Instagram, aishambuhari)

Sai dai Zango wanda har ila yau mawaki ne, wanda ke da dumbin masoya ya sake sauya sheka a ranar Talata.

"Tafiyar ta canja domin sarkin yawa ya fi sarkin karfi." Zango ya kara da cewa bayan tarbar da gwamnan jihar Kogi Bello ya yi masa.

Wasu na ganin wannan wata alama ce da ke nuna cewa an riga an fara kada gangar siyasar 2023.

A shekarun baya, ba kasafai ake ganin jaruman na Kannywood suna fitowa su nuna alkibilarsu a siyasance ba, amma a baya-baya nan lamarin ya sauya.

Akan gan su sun yi kwamba suna kai wa 'yan takara ziyara, su kuma hada kai su yi masu wakoki daban-daban, abinda kan haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG