Annobar coronavirus ta cimma wani zango na tarihi, ta yadda wandanda aka tabbatar sun kamu da cutar a duk duniya su ka kai miliyan 12, bisa ga alkaluman jami’ar Johns Hopkins dake bin diddigi game da cutar ta yanar gizo.
Adadin masu cutar Coronavirus a kasar Amurka ya zarta miliyan uku, yayin da akalla mutum 131,000 suka rasa rayukansu.
Bayan watanni da ya kwashe yana nuna rashin gamsuwarsa kan abin da ya kira "'yar amshin shatar China" da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta zama, Shugaban Amurka Donald Trump ya mika takardar sanar da ficewar kasar daga hukumar ta WHO.
Domin Kari