A ranar Laraba 8 ga watan Yuli Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da kwararrun kasar a fannin kiwon lafiya, yana mai cewa shawarwarin da suka bada akan sake bude makarantu nan da makonni masu zuwa a yayin da cutar coronavirus ke kara yaduwa“ba abu ne mai yiwuwa ba.”
Trump, wanda a ranar Talata ya hura wa gwamnonin jihohin kasar 50 da jami’an kananan hukumomi wuta akan ganin an fara zuwa makaranta kamar yadda aka saba a watan Agusta da Satumba, ya ce bai amince da ka’idojin da Cibiyar Kula da Cututtuka ta kasar ta bada ba da kuma gargadin da ta yi na cewa komawar dalibai makaranta kamar yadda aka saba na tattare da babban hadarin yada cutar.
"Yayin da suke so a bude makarantu, suna bukatar makarantun suyi wasu abubuwa da ba sa yiwuwa," a cewar Trump a shafinsa na Twitter.
Facebook Forum