Kasashen duniya na ci gaba da fadi tashin neman makarin cutar COVID-19 a daidai lokacin da kwararru a fannin kiwon lafiya ke nuna shakku kan yiwuwar samun rigakafin cutar a nan kusa, muddin idan ba a bin matakan da suka dace.
Matsananciyar guguwar nan da aka yi wa lakabi da “ISAIAS” tana kara ketawa a tsakiyar jihar New York da New England bayan ta hanzarta ratsawa a yankin tsakiyar Atlantika na Amurka, inda akalla ta kashe mutum hudu.
A jiya Talata Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya yi alkawarin ba da kariya ga masu rajin demokradiyya a Hong Kong wadanda suka tsere daga garin kuma suka la'anci China bayan da Beijing ta ce, an baiwa 'yan sanda umarnin kama masu fafutukar daga ƙasashen waje.
Jami'an Fadar White House da kuma manyan 'yan jam'iyyar Democrat a majalisar dattawa na shirin sake haduwa, bayan da bangarorin biyu sun bayyana samun ci gaba da kokarin su na yin matsaya kan sabon tallafin gwamnati na cutar coronavirus.
Matsananciyar guguwar nan da aka yi wa lakabi da “ISAIAS” tana cigaba da mamaye gabashin North Carolina.
Rahotannin da ke nuna cewa ayyukan kamfanoni a nan Amurka da ma wasu kasashe sun fara farfadowa daga annobar coronavirus, ya sa kasuwannin hannayen jarin Asia sun zaburo a yau talata.
Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa iskar Isaias wacce aka yi gargadin cewa za ta tunkari jihohin North da South Carolina za ta Iya zama karamar guguwa.
Amurka ta kai wani sabon mataki game da yadda cutar COVID-19 ke “yaduwa matuka” a yankunan karkara da birane, a cewar kwararru a fadar White House da ke sa ido akan cutar.
Kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa na Amurka Dr Anthony Fauci, ya fada wa ‘yan majalisar dokokin Amurka cewa za a samar da rigakafin cukar coronavirus nan da ‘yan watanni masu zuwa,.
Domin Kari