Kwararren likitan Amurkan nan da ya yi fice a fannin yaki da cututtuka masu yaduwa, ya ce zai yi matukar wuya duniya ta iya shawo kan cutar coronavirus wacce ya zuwa yanzu ta harbi mutum miliyan 18.8 a duk fadin duniya sannan ta kashe sama da dubu mutum 700.
Yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters a jiya Laraba, Dr. Anthony Fauci, wanda shi ne shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa, ya ce, dalilin da ya sa kwayar cutar ba za ta gushe ba, shi ne saboda yadda take da “saurin yaduwa.”
Amma ya kuma ce idan aka samar da allurar rigakafi mai inganci aka kuma mayar da hankali kan kiyaye matakan kare lafiya, akwai yiwuwar a yi nasara akan kwayar cutar.
Kwararren likitan ya kuma yi hasashen cewa har sai bayan shekara mai zuwa ne za a iya shawo kan wannan cuta – yana mai taka-tsantsan din fadin cewa, a lokacin ne mai yiwu za a samu rigakafin cutar.
Facebook Forum