Wata budurwa ta harbe kanta har lahira da wata bindiga mallakin maitaimakin babban sufeton ‘yan sanda a harabar wani ofishin ‘yan sanda da ke California, a cewar hukumomi a ranar Litinin.
Likitoci a birnin Boston na jihar Massachusetts da ke Amurka sun ce sun yi nasarar aikin dashen kodar alade da aka canzawa kwayoyin halitta a jikin wani mutum majinyaci mai shekaru 62 da ke da ciwon koda a mataki mai muni.
Idan har Majalisar Dattawa ta ki amincewa da kudurin kasafin kudin, babu makawa sai an rufe wasu ma’aikatun gwamnatin kasar.
A ranar Juma'a ne Rasha da China suka ki amincewa da wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya da Amurka ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Hamas a Gaza don kare fararen hula da ba da damar kai agajin jin kai ga Falasdinawa sama da miliyan biyu da ke fama da yunwa
Wata babban jami’ar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta shaidawa Majalisar a ranar Alhamis cewa, Amurka ba ta samu wata bukata a hukumance daga gwamnatin Nijar na ficewa daga kasar ba.
Isra'ila za ta karbe iko a Rafah ko da kuwa zai haifar da baraka da Amurka, in ji wani babban jami'in Isra'ila a ranar Alhamis, yana mai bayyana birnin Gaza mai cike da 'yan gudun hijira a matsayin sansanin karshe na Hamas mai dauke da kashi daya bisa hudu na mayakan kungiyar.
Mataimakiyar sakatarin al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, Lee Satterfield, ta bayyana haka ne a jami’ar Legas a ranar Laraba inda ta bayyana manufofin kasashen waje kan sabbin shirye-shiryen.
Zaman dardar ya karu yayin da shugaban Hamas ya zargi Isra'ila a ranar Talata da yin zagon kasa ga tattaunawar ake yi ta tsagaita bude wuta a Gaza bayan da, a karo na biyu, Isra’ilar ta kai farmaki a asibiti mafi girma a yankin Falasdinu da ya daidaice.
A yau Litinin Donald Trump ya gaza samun takardar shaidar da za ta ba shi damar daukaka kara kan hukuncin dala miliyan 454 da aka yanke wa tsohon shugaban na Amurka a wani zambar a birnin New York ba tare da damar tura kudin da kansa ba, a cewar lauyoyinsa.
A ci gaba da kwan gaba kwan baya da huldar Jamhuriyar Nijar da wasu kasashen Yamma ke yi, kasar da ke karkashin mulkin soji, ta yi shelar yanke huldar soji da Amurka.
Domin Kari