Kawo yanzu dai babu wani mataki na karshe kan ko dukkan sojojin Amurka za su fice daga Nijar da Chadi ko kuma a'a, kasashen Afirka biyu da ke da muhimmanci ga kokarin da sojoji ke yi na dakile kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a yankin Sahel.
Wasu jami'an Amurka biyu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters a ranar Talata cewa Amurka na shirin bayar da tallafin soji na dala biliyan 1 ga Ukraine, wanda shi ne na farko da za a samu daga kudirin dokar Ukraine da Isra'ila da ba a sanya wa hannu ba tukunna.
Kasashen duniya sun yi kira ga Isra'ila da ta takaita ayyukanta a birnin Rafah da ke kan iyaka da kudancin kasar, inda miliyoyin 'yan gudun hijira suka fake.
Wani zakaran dara na wasan Chess, ‘dan Najeriya kuma mai fafutukar koyar da ilimin yara yana kokarin buga dara na tsawon sa'o'i 58 ba tare da tsayawa ba a dandalin Times Square na birnin New York domin karya tarihin duniya na tsawon wasan chess mafi dadewa.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya shirya wani taro da nufin samar da daidaito tsakanin maza da mata, da kuma yadda za a karfafa mata. Ya kuma duba yadda ‘yan jarida ke ba da rahotannin abubuwan da suka shafi mata.
Donald Trump ya zama tsohon shugaban kasar Amurka na farko da zai fuskanci shari'ar aikata laifuka a ranar Litinin, a lokacin da za a fara zabar masu taya Alkali yanke hukunci a kotun Manhattan, a shari'ar tuhumar biyan kudin toshiyar baki ga taurariyar fina finan batsa Stormy Daniels.
Mai magana da yawun fadar White House a fannin tsaro, John Kirby ya shaidawa gidan talabijin din CNN cewa "galibin makaman da aka harba ta sama, daga Iran aka harba su.
OJ Simpson ya kasance 76
Cibiyar samar da zaman lafiya ta Amurka ta bayyana cewa. dole ne Amurka ta inganta huldar kasuwanci da kasashen Afirka domin dakile dogaro ga kasar China wajen samun ma'adanai masu mahimmanci.
A jihar New York, hazo ya dan kawo cikas ga masu kallon kusufin amma a jihar Texas da sauran wuraren da lamarin ya auku, an ga kufusin na dan wasu mintina yayin da wata ya ratsa ta tsakanin rana da duniyar dan adam.
Wani rahoton Hukumar Kula da Duwatsu (USGS) ta Amurka ya bayyana cewar, da safiyar Juma'ar nan, wata girgizar kasa ta afkawa yankin arewa maso gabashin birnin New York mai yawan jama'a, inda mazauna yankin suka bada labarin jin motsin kasa, al'amarin da basu saba ji ba.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada wa Firan ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Alhamis cewa ci gaba da samun tallafin Amurka a yakinta da Hamas zai bukaci ta bijiro da matakan kariyar da za su yi amfani da su don kare fararen hula da ma’aikatan jin-kai da ke yunkurin kai musu abinci.
Domin Kari