Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wani gida a birnin Gaza da ke kudancin kasar ya kashe akalla mutane 9, shida daga cikinsu yara ne, a cewar hukumomin asibitin yankin a ranar Asabar, wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kusan tsawon watanni bakwai a yankin na Falasdinawa da ta yi wa kawanya.
Yakin da Isra'ila ke yi da kungiyar mayakan Hamas ya haddasa fargaba a yankin gabas ta tsakiya da ke fama da rikice-rikice.
Harin da aka kai da yammacin ranar Juma'a ya shafi wani gini da ke yammacin yankin Tel Sultan a birnin Rafah, a cewar jami'an tsaron farin kaya na Gaza. An kai gawarwakin yaran shida, da mata biyu da namiji daya zuwa asibitin Abu Yousef al-Najjar da ke Rafah, kamar yadda bayanan asibitin suka nuna.
A asibitin ‘yan uwan mamatan sun yi ta kuka tare da rungumar gawarwakin yaran, da aka nade da farin kyalle, yayin da wasu suka yi ta jajanta musu.
A yayin wani taron manema labarai ranar Juma’a, a wurin taron kungiyar kasashen G-7 da aka yi a kasar Italiya, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fadi cewa gwamnatin Biden "ba za ta goyi bayan wani gagarumin farmakin soja a Rafah ba."
Dandalin Mu Tattauna