Binciken ya yi kiyasin cewa tsakanin watan Oktoban 2023 zuwa Yunin 2024, an sami mutuwar Falasdinawa sama da 64,000 sakamakon tashin hankali a Gaza, wanda ke nuni da cewa ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke yankin, ta rage a rahoton adadin da ta bayar na wadanda suka mutu da kusan kashi 41%.