Wannan shine karo na 6 da ake shirya babban zabe a Jamhuriyar Nijar, tun bayan da kasar ta tsunduma tafarkin dimokaradiyya a 1991, lokacin da kungiyoyin fafutukar kasar suka kawo karshen mulkin shekaru 16 da Janal Ali Saibou ya gada daga marigayi Janal Seyni Kountché.
Yayin da yan kasar Nijar da dama ke zaune a Najeriya, musammam a makwabtan jihohi irin su Sokoto da Kebbi da Zamfara, suka koma gida domin gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisar Dokoki, wasu da yawa suna jiran jefa nasu kuri’un a Najeriya.
Babban taron muhawara na kasa da ake kira conférence nationale, na ranar 29 ga watan Yuli na shekara ta 1991, shine ya bada damar girkuwar tafarkin dimokaradiyya a jamhuriyar Nijar, wanda hakan ya bada damar bayyanar jam’iyyun siyasa daban daban.
A ranar 21 ga watan Fabarairu ne za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko hade da na 'yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar, za kuma gudanar da zagaye na biyu a ranar 28 Maris.
A jamhuriyar Nijar an rufe yakin neman zabe a jiya Juma’a, kan haka ne ma ‘yan takarar zaben shugaban kasa suka shirya gangamin karshe domin kara tallata manufofinsu ga ‘yan kasar da nufin jan ra’ayin mutane.
Muryar Amurka ta shirya wani taron tattaunawa a birnin Yamai, karkashin jagorancin Ibrahim Ka-Almasi Garda, game da yadda za a gudanar da zaben ranar 21 ga wannan wata na Fabarairu.
A yayin da ake rufe kyamfe na bana a kasar Nijar, shugaba mai ci Mahamadou Issoufou, dan takarar jam'iyyar PNDS, yayi gangami a birnin Konni
A yayin da kasar Nijar ke shirin zaben shugaban kasa da 'yan majalisu 'yan kasan na korafin rashin cin gajiyar anfani albarkatun kasa da Allah ya yi masu to ko me ya kawo hakan? Akwai bayani.
Domin Kari