Shugabannin kungiyoyin 'yan Najeriya suna farin ciki da ziyarar aiki da shugaba Buhari ya kawo Amurka.
Tsohon jakadan Najeriya a kasar Spain Ambasada Yaro Yusuf Mamman, yace gayyatar shugaba Buhari zuwa Amurka karfafa demokuradiyya ne.
A yau Lahadi 19 ga Yulin 2015 ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara ziyarar aiki ta kwana 4 zuwa birnin Washington a nan Amurka don ganawa da Shugaban Barack Obama.
Ranar lahadin nan ne ake sa ran shugaban na Najeriya zai fara ziyarar aiki na kwanaki hudu
Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka Tony Blinken yayi taron manema labarai a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja.
Sabon shugaban Najeriya zai gana da shugaba Barack Obama na Amurka a wata mai zuwa domin tattauna yaki da kungiyar Boko Haram da wasu muhimman batutuwan.