A dai-dai wannan lokaci da zanga-zangar Cibok ke cigaba da wakana a sassa daban-daban na duniya, shuwagabanni mata sun fara tofa albarkacin bakinsu ganin yadda babu labarin wadannan yara su sama da 200 da aka sace, makonni uku kennan.
A dai-dai lokacin da jama’a a duk fadin duniya suke mayar da hankulansu akan daliban Cibok da aka sace su sama da 200 a makarantarsu ta Sakandare makonni uku da suka wuce, kasar Kamaru na musanta zargin da akeyi na cewa an ketara da wasu daliban zuwa cikinta, domin a sayar da su.
A cigaba da juyayin sace daliban makarantar 'yan mata dake Cibok a jihar Borno gamayyar daliban jihar sun kira dalibai a duk fadin duniya da su kauracewa azuzuwa gobe domin yin alhini sabili da 'yan matan da har yanzu ba'a ganosu ba.
Yayin da ake cigaba da juyayi da mayar da kalamun bacin zai dangane da daliban da aka sace a makarantar mata dake Cibok, matan Legas sun fito sun yi zanga-zangar lumana domin a sako daliban.
Amurka tayi tanadin matakai domin taimakawa wajen nemo dalibai 'yan makarantar Cibok da aka sace makonni uku da suka wuce, su sama da 200.
Mai dakin shugaban Najeriya, Patience Jonathan ta zargi da hannun Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima a sace dalibai mata sama da 200 da akayi a makarantar Sakandare dake Cibok, Jihar Borno.
A dai-dai lokacin da aka share makonni uku da sace dalibai mata sama da 200 a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok, Majalisar Dokokin Jihar Borno ta dorawa Shugaba Goodluck Jonathan alhakin sace yaran.
Biyo bayan ganawar da tayi da matar Shugaban Kasa Mrs. Patience Jonathan, hukumar ‘yan sandan farin kaya wato SSS ta tsare shugabar matan Cibok a birnin Abuja, Naomi Nyadar.
Har yanzu ana ta ci gaba da samun kiraye-kiraye ga shuwagabanni da masu ruwa da tsaki a jagorancin Najeriya da su dukufa domin nemo dalibannan da ke ci gaba da garkuwa da su wadanda aka diba daga garin Cibok.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bada umarni ga manyan jami’an tsaron kasa akan suyi ‘duk abinda zasu iya yi’ domin ceto dalibai sama da 200 mata da aka sace a watan da yace.
Kungiyar matasan arewa ta tsayar da lokacin da zata yi gangami zuwa dajin Sambisa domin kwato daliban da aka sace indan har gwamnati ta kasa kwatosu.
Musulmai mabiya darikar Tijjaniyya sun hallarci addu’ar da aka yi a sabon Masallacin Juma’ar Sabon Gari dake Jalingo a Jihar Taraba, karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauci, daya daga cikin manyan malaman Najeriya.
Domin Kari