Biyo bayan bidiyo da Boko Haram ta fitar akan daliban da ta sace Marylin Ogah mai magana da yawun 'yan sandan leken asiri ko SSS tace shugaban kungiyar Boko Haram na yanzu ba Abubakar Shekau ba ne.
Yayin da mata a koina a Najeriya ke cigaba da gangami a sassa daban daban dangane da daliban da aka sace, a jihar Nasrawa 'yan sandan jihar sun gurfanar da wani dan jarida a gaban kotu domin ya rubuta rahoto inda ya nuna 'yan sanda mata sun shiga gangamin da mata 'yan uwansu suka yi.
Kungiyar matan Najeriya reshen jhar Yobe ta bi sawun takwarorinta inda ta mika wasikar neman a sako daliban Chibok ga gwamnan jihar Ibrahim Geidam.
Biyo bayan fitar da wani bidiyo dauke da 'yan matan da aka sace kungiyar Boko Haram tayi tayin sako wasu 'yan matan idan har gwamnati ta yadda ta sako 'yan kungiyar dake tsare.
Bayan wata daya da sace daliban makarantar 'yan mata dake Chibok a kudancin jihar Borno har yanzu shugaban kasar ya kasa ziyarar garin
aka nemi dattawa na kirki gwamnati ta sasu a kwamiti a nemi mutane nan a zauna dasu saboda sako yaran nan", a cewar wani mazaunin Jihar Borno.
A wani sabon bidiyo da mutumin da yace shine shugaban kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, ya fitar a baya-bayannan, Abubakar Shekau yace ya musuluntar da wadannan mata, wadanda yace ya sato su, sannan yana bukatar ayi musaya dasu.
Biyo bayan taron tattalin arzikin duniya da aka kammala a Abuja ofishin jakadancin Akyurka ya shirya wani taron na 'yan kasuwa da wasu gwamnonin Najeriya.
Yayin da 'yan jam'iyyar APC suka kaiwa gwamnan jihar Borno gaisuwar jajantawa sabili da daliban Chibok da aka sace gwamna Shettima yace idan sadakar da ransa zai kawo wa al'ummarsa da kasar zaman lafiya to ashirye yake yayi hakan.
Amincewar da shugaba Jonathan ya yiwa sojojin kasashen waje su shigo domin su taimaki kasar gano daliban da aka sace ya sa wasu suna kiran shugaban yayi murabus daga mukaminsa.
Masu zanga-zanga a cikinsu harda tsohuwar Ministan Ilimi, sun jaddada ‘yancinsu na gudanar da taron lumana, yayin da suke kira a dawo da dalibai su sama da 200 da ‘yan bindiga suka sace.
A wannan lokaci da duniya take zuba idanu domin gani hukumomin Najeriya tare da agajin kasashen turai sunyi kokarin ceto daliban Cibok, 'yan siyasa har yanzu bakinsu bai bar kumfa ba, saboda Senata John McCain daga Amurka ya nuna fusatarshi akan gwamnatin Najeriya da ta bari aka sace dalibai.
Domin Kari