Yayin da jami’an kasa da kasa suka riga suka fara isa Najeriya domin taimakawa wajen gani an ceto daliban Cibok, mafi yawancin gwamnoni da shuwagabanni basu ce komai ba game da lamarin, musamman ma ta bangaren nuna alhini da jajantawa mutanen Najeriya.
Daga cikin matakan da shuwagabanni suke dauka a lokutan tashin hankali da rigingimu, akwai ziyarar gani da ido, domin jajantawa da nuna alhini. Tambayar anan itace yaushe Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya zai je Cibok?
Sheikh Abdul’aziz al-Sheikh na Saudiyya yace an kafa kungiyar ta Boko Haram ne kawai domin a bakanta sunan Musulunci.
A wani matakin ba-sabam ba, Mes. Obama ta gabatar da jawabin mako-mako na shugaban inda ta maida hankali kan sace dalibai mata na Chibok su fiye da 300.
Majalisar Fiqhu ta Duniya da Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Kungiyar Kasashen Musulmin Duniya sun yi tur da sace 'yan matan Chibok da kalamun Shekau
A lokacin da yake tarbar gungun masu gangamin neman gwamnati ta dauki kwararan matakai domin ceto dalibai mata sama da 200 da aka sace a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok, gwamnan Jihar Lagos Babatunde Fashola ya bayyana matsayinsa.
Rahotanni daga Jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai wani hari a garin Liman Kara, yankin karamar hukumar Madagali dake makwabtaka da jihar Borno, inda suka yi amfani da bama-bamai wajen kona gidaje da ruguza wata babbar gada.
Shugaban ECOWAS a halin yanzu, kuma shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya shiga sawun shugabanni masu neman taimakawa Najeriya saboda hakkin makwabtaka, da kuma matsayinsa na Shugaban ECOWAS a halin yanzu.
Barrista Solomon Dalung na kungiyar Dattawan Arewa yace yanzu haka ma, kungiyoyin sa kai wadanda suka hada Gidauniyar Dalung sun fara tattara bayanai domin gurfanar da gwamnatin Najeriya a kotun bin Kadin manyan laifuka ta duniya, wato ICC.
Yunkurin hadakar kungiyoyin mata da matasan da suka zaman dirshen domin nuna damuwarsu game da tabarbarewar tsaro a Najeriya ya samu cikas, biyo bayan haramta taron da hukumar jami’an tsaro Farin Kaya a Jihar Kaduna tayi.
Jami’an tsaron Najeriya sunce suna da isassun kayan aiki na amfani da su wajen neman daruruwan dalibai mata wadanda aka sace daga makarantarsu ta Sakandare a Cibok.
Rahotani na nuni da cewa hankali ya fara kwanciya a garin Chibok ganin yanda yawan jami'an tsaro ya karu a garin
Domin Kari