Akasarin manyan hanyoyin mota da suka shiga ko suka fita daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun zamo masu hatsarin gaske ga matafiya. Direbobi sukan yi gudu sosai, yayin da ba a cika ganin motoci kamar da ba a kan hanyoyin. Wannan hanyar Kano ce daga Maiduguri kafin a kai garin Beni Sheikh.