Rahotanni na cewa mayakan Boko Haram dake rike da wasu sassan jihar Adamawa sun canza salo inda suka shiga sace mata da matasa masu jini a jika.
Cibiyar kare hakin bil Adama da tallafawa jama'a ta kira shugaba Jonathan ya tasa keyar kwamitin da ya kafa domin tallafawa jama'ar da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu a jihohin Adamawa, Borno da Yobe da ma wasu wurare.
Kungiyar Jumnata Fulbe ba kishiyar Miyetti Allah ba ce
Rundunar sojojin Najeriya ta gaskata rahotannin dake cewa wani jirgin saman yaki na kasar da ya tashi daga Yola domin gudanar da shawagin aiki ya bace tun jiya babu labarin abinda ya same shi.
A Nijerya an cigaba da kiraye kirayen gwamnati ta dau mataki kan wadanda Baturen Australia din nan mai suna Stephen Davis ya zarga da taimakawa 'yan Boko Haram.
Ga dukkan alamu sojojin Nijeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram a garin Konduga, su ka kashe na kashewa tare da kwace muggan makamansu. Wannan ya kwantar ma mazauna birnin Maiduguri da kafin nan ke fargabar yiwuwar 'yan bindigar su abka ma birnin
‘Yan kungiyar Boko Haram, a yanzu haka sun mamaye gidajen, wasu fitattun mutane a yankin Gulak da Madagli, ciki har da gidan mukaddashin gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, da kuma na Hakimin Duhu.
Yanzu haka dubban 'yan Najeriya ne suka ketara iyaka suka shiga kasashen Chadi da Niger da Kamaru daga jihar Borno dake fama da farmakin kungiyar Boko Haram tare da kwace kauyuka da garuruwa da fafattakar sojojin Najeriya a wasu wurare..
Bisa ga alamu da shaidun ganao har yanzu garin Bama yana hannun 'yan Boko Haram kusan kwana goma sha daya ke nan
Wani tsohon gwamnan soja a Jihar Kaduna, kuma jigo a kungiyar kare muradun yankin arewacin Najeriya.
Gwamnati ce Yakamata ta Samarwa Sojoji Makamai.
Yaki tsakanin 'yan Boko Haram da sojojin Najeriya da yake kara yinkamari ya sa gwamnatocin jihohin arewa maso gabas su fara fargaban barkewar yunwa a yankinsu.
Domin Kari