Bayanai na nunawa cewa wasu 'yanbindiga suka yiwa wasu mutane kwantar bauna akan hanyarsu daga Wukari zuwa Ibi
Rahotannin baya-bayan nan na nuna cewa adadin wadanda su ka mutu a hare-haren da aka kai Bauchi da Gombe 26 ne, banda wadanda su ka sami raunuka.
An kai hari kan wani bikin aure a Karamar Hukumar Gasol ta jihar Taraba, inda aka hallaka mutane 10.
'Yansandan jihar Taraba sun dauki tsauraran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a a lokutan bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara
Da dumi duminta, wani bom ya tashi a wata kasuwa a jihar Bauchi amma ba a san adadin wadanda suka mutu ko jikkata ba.
Rikicin jihar Nasarawa tsakani kabilu, yayi sanadiyar daidata al'ummar wasu garuruwan, wanda ke gudun hijira yanzu haka. abinda wasu ke gani hakan zai iya shafar zabe mai zuwa a jihar.
Karo na biyu ke nan ana tada Bom a tashar mota a jihar Gombe wanda ya janyo hasarar rayuka da raunata mutane da dama.
Yayin da ake hidimar shirya bikin kirsimati da na sabuwar shekara wasu shugabannin sun bukaci a yi anfani da bikin a kawar da banbancin addini da na kabilanci domin a samu zaman lafiya a jihar Adamawa
Kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula sun zamo ruwan dare a yankin arewa maso gabashin Najeriya a dalilin hare-haren ‘yan Boko Haram. A yayin da wannan tashin hankali ke bazuwa zuwa wasu sassan na Najeriya, har ma da makwabtanta, fargaba tana kara yawaita cewa watakila gwamnatin Najeriya ba ta san yadda zata takali wannan batu ba. Ko kuma tana kara rura wutar fitinar ne ma da kanta.
Domin Kari