Wani hatsarin jirgin sama ya kashe mutane akalla 68, a cewar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Nepal.
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wani dan kasar Iran kuma dan kasar Birtaniya.
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), jiya Laraba ta ce tana kira ga kasar China, da ta yi karin bayani kan yaduwar da cutar COVID-19 ke yi a kasarta.
Jami'an 'yan sanda sun cafke wani dan kasar Libiya mai shekaru 29 mai jagorantar safarar bakin haure da ke bi ta Nijar zuwa Turai.
Wasu ‘yan bindiga ne suka harbi shugaban majalisar dattawan Haiti Joseph Lambert a ranar Lahadi a wata unguwa da ke kusa da ginin majalisar dokokin kasar a birnin Port-au-Prince.
Masu goyon bayan tsarin Jamhuriyar Musuluncin Iran sun kona tutocin Faransa a wajen ofishin jakadancin Faransar da ke birnin Tehran, inda suka yi zanga-zangar nuna adawa da wani zanen barkwanci da mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta wallafa kan shugaban addinin Iran.
Yau aka yi jana’izar Fafaroma Emeritus Benedict na 16, wanda ya rasu yana da shekaru 95 a ranar 31 ga watan Disamba, a birnin Vatican, bayan nan magajinsa Fafaroma Francis zai shugabanci wata hidima da za a gudanar.
An tura tawagar wakilai daga gwamnatin Italiya da Jamus, wato kasar Paparoma Benedict ta asali.
A ranar Talata majalisar ta kada kuri’a sau uku ba tare da samun nasara ba, lamarin da ya kai ga aka dage zaman zuwa Laraba.
Dan Republican Kevin McCarthy mai wakiltar jihar California da ke takarar kujerar, ya gaza samun adadin kuri’a 218 da ake bukata a zagaye uku da aka yi.
McCarthy na fatan ganin ya gaji Nancy Pelosi ‘yar Democrat amma kuma yana fuskantar kalubalen rashin samun goyon baya - har daga abokansa.
A daidai lokacin da ake shirye-shiryen jana’aizar Fafaroma Benedict mai ritaya, an bayyana kalaman karshe da ya furta kafin komawarsa ga mahalacci.
Domin Kari