Paparoma Francis, wanda bai gama murmurewa daga rashin lafiya ba, ya bi shawarar likitocinsa inda ya tsallake bikin ranar Juma’a wato ‘Good Friday Night’ wanda akan kwashe sa’a biyu ana yi.
Adadin matan da ke take dokar saka hijabi a Iran na ci gaba da karuwa a ‘yan kwanakin nan, tun bayan jerin zanga-zanga da aka yi a lokacin mutuwar wata Bakurdiya ‘yar shekara 22 mai suna Mahsi Amini, wacce aka zarga da keta dokar.
Justine Jones da Justine Pearson sun yi bore ne kan neman majalisar ta dauki matakan dakile hare-haren bindiga, sai dai hanyar da suka bi wajen gabatar da korafinsu ta sabawa dokar majalisar.
An ji karar tashin bama-bamai masu karfi a wasu sassan Gaza yayin da jiragen yakin Isra'ila suka kai farmaki kan wuraren da sojoji suka ce hanyoyin karkashin kasa ne da wuraren kera makaman Hamas.
Mutane biyu ne suka mutu yayin da sama da miliyan guda suka rasa wutar lantarki a ranar Alhamis, bayan da dusar kankara ta afka wa larduna biyu mafi yawan jama’a a kasar Canada, gabanin hutun karshen mako.
A Amurka, babu wata doka da ta hana wani da ake tuhuma ko aka samu da laifi tsayawa takarar shugaban kasa ko rike mukamin.
Trump zai zama tsohon shugaban Amurka na farko da za a tuhuma da laifi, lamarin da ba a taba gani ba a tarihin kasar.
Bulgariya ta kamala dukkanin shirin tattaunawa mai tsawo da sarkakkiya a game da kafa gwamnatin rikon kwarya bayan da aka aka kamala gudanar da zabe sau 5 cikin shekaru 2 inda aka gaza samun wanda yayi nasara.
Da yawa daga cikin ‘yan Republican da shi kansa Trump sun kwatanta wannan shari’a a matsayin bi-ta-da-kullin siyasa.
An gano gawarwakin mutane 36 a cikin wata rijiya a wani wurin ibada na mabiya addinin Hindu da ke tsakiyar Indiya bayan da mutane da yawa da ke halartar wani biki suka fada cikin tabo a lokacin da murfin rijiyar ya rufta, a cewar jami'ai ranar Juma'a.
Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan ya nada babban dansa Sheikh Khaled a matsayin yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, babban birnin kasar mai arzikin man fetur a yankin Gulf, tare da nada 'yan uwansa a kan manyan mukamai.
Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen ta ce duk wani “matsin lamba daga waje,” ba zai hana tsibirin mai cin gashin kan sa mu’amala da sauran duniya ba.
Domin Kari