Kamfanin dillancin labaran Rasha ya rawaito cewa mataimakin firaministan kasar, Alexander Novak ya fada a cikin wani jawabin da ya wallafa a yau Laraba cewa, rabin yawan albarkatun man fetur din da Rasha ta fitar a cikin wannan shekarar ta 2023 ta tura shi China ne, yayin da kason Indiya ya karu cikin shekaru biyu zuwa kashi 40 cikin 100.
Alexander Novak, wanda ke kula da sashen makamashi na Rasha ya ce, "Babban abokan hulda a halin da ake ciki yanzu su ne China, wadda kasonta ya karu da kusan kashi 45% zuwa 50%, sai kuma Indiya."
"Tun da farko, ba a sami wadataccen man ga Indiya ba a cikin shekaru biyu, amma jimillar kason man da Indiya ke samu ya kai kashi 40%.
Dandalin Mu Tattauna