Yayin guguwar, iska mai karfin gaske ta ka da bishiyoyi sannan ambaliyar ruwa ta ratsa kauyuka tare da yin awon gaba da gidaje.
Wasu jerin hare-hare da jiragen yakin Isra'ila suka kai kudancin Lebanon sun kashe mutane 16, yayin da wasu rokoki da kungiyar Hezbollah ta harba ta yi sanadiyyar mutuwar wani Ba'isra'ile daya, wanda ya zamar da ranar Laraba nan mafi muni cikin sama da watanni biyar na gwabza fada a kan iyakar kasar
Jiya Laraba kasar Ireland ta ce za ta shiga tsakani a karar Isira’ila da Afurka Ta Kudu ta yi kan zargin kisan kiyashi, a wani mataki na nuna alama mai karfi kan damuwarta game da aika-aikar Isra'ila a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba.
Dangantaka tsakanin Shugaba Joe Biden da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta fara yin tsami ne a Litinin bayan da Amurka ta amince da kudirin tsagaita wuta a Gaza a taron Majalisar Dinkin Duniya tare da kakkausar suka daga Shugaban na Isra'ila.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kudirin neman a tsagaita wuta a gaza nan take, a karon farko tun bayan barkewar rikicin bayan da Amurka ta kauracewa hawa kujerar naki.
Isra'ila ta fadawa wasu kasashen Turai hudu a yau Litinin cewa shirinsu na yin aiki don amincewa da kafa kasar Falasdinu ya zama "daukaka wa ta'addanci" wanda zai rage damar yin shawarwari na kawo karshen rikicin da ke tsakanin makwabtan.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce dakarun Isra'ila sun yi wa wasu asibitoci biyu kawanya a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi ta luguden wuta kan jami'an kiwon lafiya, daga bisani Isra'ila ta ce ta kama 'yan ta'adda 480 yayin da aka ci gaba da gumurzu a babban asibitin Al Shifa na Gaza
Wasu mutane hudu da ake zargi da kai harin a dakin raye-raye da wake-wake na kasar Rasha da ya kashe mutane sama da 130 sun gurfana a gaban kotu a birnin Moscow jiya Lahadi bisa zargin ta’addanci.
A yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasar Senegal da rikicin siyasa ya dabaibaye a baya-bayan nan, wasu ‘yan kasar da suka tsere zuwa Turai sun ce, suna fatan komawa gida doń a dama da su a ceto tattalin arzikin kasar da ke barazanar durkushewa.
Amurka ta gargadi Rasha akan cewar mayakan kungiyar ISIS nada niyar kai hare-hare cikin kasar 'yan kwanaki gabanin maharan su afkawa gidan rawa na "Crocus City Hall" a wani hari da yayi sanadiyar mutuwar gwamman mutane saidai Shugaba Vladimir Putin yayi watsi da shawarar a matsayin "takalar fada".
A ranar Asabar Rasha ta ce ta kama mutane 11 - ciki har da ‘yan bindiga hudu, kan harin da aka kai a wani zauren raye-raye na Moscow da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 115.
Gimbiyar Wales ta sanarda cewar ta kamu da cutar sankara, harma an fara yi mata magani, inda ta bukaci al'umma su bata lokaci da wuri ta kammala samun waraka a killace.
Domin Kari