Hakan na zuwa ne bayan da kungiyar Hezbollah ta kai wasu jerin hare-haren ta sama kan Isra’ila da jirage mara matuki.
Da alamar da mai masaukin baki a gasar Olympic ta 2024, wato Faransa, ba za ta sha kunya ba, ganin ta samu hayewa zuwa buga wasan kwallon kafa na karshe.
Kasuwannin hannayen jari a fadin duniya na tangal tangal, yayin da ake fargabar tsunduma cikin matsalar tsananin tsadar kaya musamman ma a manyan kasashe irin Amurka da Japan da sauransu
Hotunan bidiyo sun nuna yadda dubban mutane suke ta bazama akan titunan Dhaka, babban birnin kasar suna nuna farin cikin saukar firaiministar wacce ta kwashe shekaru 15 tana mulkar kasar.
Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon ta ce ta kaddamar da wani harin jirgin sama mara matuki a safiyar yau Litinin a arewacin Isra'ila, inda sojojin Isra'ila suka ce harin ya raunata dakarunta biyu tare da ta da gobara.
Nemour ta samu damar fafatawa a karkashin tutar Algeriya ne bayan da kungiyarta ta samu sabani da hukumar wasannin tasalle-tsallen Faransa ne.
Masu zanga-zanga sun kai hari kan 'yan sanda tare da tada wuta a birnin Sunderland da ke arewa maso gabashin Burtaniyya a ranar Juma'a yayin da tashin hankalin ya bazu zuwa wani garin a arewacin kasar, biyo bayan kisan wasu yara uku a ranar Litinin a Southport.
Wasu ‘yan Najeriyar mazauna wasu kasashe da ke bibiyar al’amuran da ke gudana a kasar da dama sun yarda cewa matsin rayuwar da jama’ar kasar ke fama da ita, wani abin tashin hankali ne da aka jima ba a duba wa ba.
A yau Laraba, Shugaban Turkiyya Recef Tayyib Erdogan, ya yi Allah-wadai da mummunan kisan gillar da aka yiwa amini kuma 'dan uwansa, shugaban kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa Musulmai ta Hamas, Isma’il Haniyeh.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani a sakon ta’aziyya da ya aika kan kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh, ya bayyana cewa za su dauki fansa kan kisan da aka yi wa Haniyeh.
Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka ta fada a ranar Talata cewa, tana shirin kashe dala miliyan 10 don dakile kamuwa da cutar murar tsuntsaye tsakanin ma’aikatan gona, da ya hada da dala miliyan 5 don rigakafin mura na lokaci-lokaci.
Domin Kari