Sallamar ta Mourinho na zuwa ne bayan da ya kwashe wata 17 yana horar da 'yan wasan na Hotspur.
Yanzu haka masoya kwallon kafa a duk fadin duniya, musamman a shafukan sada zumunta, na ta tafka muhawara kan kungiyoyin da za su kai wasan karshe a wannan gasa.
A yau Laraba Real Madrid za ta bi Liverpool gida, don karawa a zagaye na biyu a ci gaba da gasar neman lashe kofin Champions League na UEFA yayin da Dortmund za ta karbi bakuncin Manchester City.
“Yau mun samu takarda daga hukumar da ke gudanar da wasanni ta Premier League a Najeriya cewa, sun yarda, shi ma Ahmed Musa ya amince cewa zai sake dawowa ya yi wasa a League din Najeriya,”
‘Yan wasan Ronald Koeman sun yi amannar an danne musu bugun fenarti a lokacin da aka ka da Martin Braithwaite, bayan wata shigar karfi da suke zargin Ferland Mendy ya yi masa.
Vinicius Junior ya ci wa Real Madrid kwallo biyu, a karawar da suka yi da Liverpool a neman lashe kofin gasar zakarun turai ta Champions League.
Pep Guradiola ya caccaki hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA saboda rashin hutun da ba sa ba ‘yan wasa. Yanzu haka Manchester City na kokarin ganin ta lashe gasa hudu a wannan kakar wasa ta bana. A cewar manajan kungiyar ta City, ‘yan wasansa mutane ne ba na’urori ba.
Madrid za ta je wasan ne da zaratan ‘yan wasa 21, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.
Dan wasan kungiyar kwallon kafar Leicester City, Kelechi Iheanacho ya tswaita zamansa a kungiyar da shekara uku.
A ranar 6 ga watan Afrilu, Real Madrid za ta gwada kaiminta da Liverpool a zagayen farko na wasannin kusa da na karshe a gasar ta UEFA.
Dan wasan tsakiya na kungiyar Napoli, Victor Osimhen ne ya fara zura kwallo kafin a je hutun rabin lokaci.
Domin Kari