Ronaldo ya ci dukkan bugun fenariti 18 da ya yi a baya ga Al-Nassr, amma a wannan karon ya cilla ta saman raga.
Madrid da 'yan wasanta baki daya ba su halarci bikin ba, sannan sun shiga shafukan sada zumunta sun rubuta kalaman da suka nuna bacin ransu saboda ba a zabi Vinicius Jnr ba.
Sanarwar ta kara da cewa Ruud van Nistelrooy zai maye gurbin Ten Hag a matsayin kocin rikon kwarya tare da sauran ma'aikatan da suka yi aiki tare da tsohon kocin.
Jaridar kwallon kafa ta France Football ce ta kirkiri ba da wannan lambar yabo a shekarar 1956 don karrama dan kwallon da ya fi nuna bajinta a fagen tamaula.
Bikin mika kyautar ta CAF zai gudana ne a birnin Marrakech na kasar Morocco, a ranar 16 ga watan Disamba mai zuwa.
Kungiyar ta Najeriya, wacce ta lashe kofin Afirka sau uku, tana matsayi na 39 a duniya a baya.
Ana sa ran dan wasan gaban na Madrid wanda dan asalin kasar Brazil ne zai yi wasu gwaje-gwaje kafin wasan gida na ranar Asabar.
Wata majiya a kungiyar ta Leverkusen ta ce Boniface yana cikin koshin lafiya bayan aukuwar hatsarin.
A jiya Laraba Najeriya ta fara gasar cin kofin duniyar mata ‘yan kasa da shekaru 17 inda ta lallasa tawagar kasar New Zealand da ci 4 da 1.
Sabon mukamin tsohon kociyan kungiyar Chelsea zai fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.
A ranar Litinin, kungiyar kwallon kafa ta maza ta Najeriya ta janye daga wasan da za a yi a Libya, inda ta nuna fushinta kan yadda aka yashe su a filin jirgin sama bayan da aka karkata akalar tafiyarsu
Domin Kari