Lookman wanda ke taka leda a kungiyar Atalanta dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ya dauki hankula bayan da ya zura kwallaye 3 a wasan karshe na gasar Europa wacce kulob din nasa ya lashe.
Haka kuma tawagogin kwallon kafar Najeriya; Super Eagles ta maza da takwararta Super Falcons ta mata na cikin rukunin tawagogi 3 na karshe da aka fitar a jiya Alhamis dake neman lashe kyautar gwarzuwar tawaga ta bana.
FIFA ta kuma amince da gasar cin kofin duniya na shekarar 2030, wanda za a gudanar a kasashe shida kuma a nahiyoyi uku, inda za a gudanar da wasanni uku na farko a Argentina, Paraguay da Uruguay.
An sanya kungiyar Palmeiras ta kasar Brazil da takwararta ta kasar Portugal Porto a rukunin “A” tare da kungiyar Inter Miami ta jagoran cin kofin duniya dan kasar Argentina Messi wanda FIFA ta bata gurbi bayan da ta yi zarra a gasar MLS ta wannan kakar.
Ademola Lookman, William Troost-Ekong, Paul Onuachu da Asisat Oshoala su ne ‘yan Najeriyar da suka shiga jerin ‘yan wasan da aka tsamo don neman kambun a matakai daban-daban.
Lampard ya maye gurbin Mark Robins, wanda aka sallama a farkon wannan watan.
Yayin da wasu tawagofin suka samu cancantar shiga gasar tunda fari, saura irinsu Jamhuriyar Benin sun samu nasu tikitin shiga gasar ne a kurarren lokaci.
A yayin dan wasan gaban Najeriya Ademola Lookman ya samu shiga cikin gwaraza 5 din, jagoran tawagar kasar, William Troost-Ekong bai samu shiga cikin jerin sunayen mutum 9 na farko ba.
Fafatawar da Jamhuriyar Benin a filin wasa na Felix Houphouet Boigny zata gudana ne a ranar 14 ga watan Nuwamba da misalin karfe din dare agogon Najeriya, yayin da fafatawar rana ta 6 da kasar rwanda zata gudana a filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo a ranar 18 ga watan Nuwambar da muke ciki.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce babu kamshin gaskiya a labarin.
Dan kasar Portugal mai shekaru 39, Ruben Amorim, wanda zai koma Old Trafford daga klub dinsa na Lisbon Sporting a ranar 11 ga Nuwamba, ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa watan Yunin 2027.
Domin Kari