Yanzu Liverpool na da maki 70 yayin da Arsenal ke biye da ita da maki 68.
Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewar, an shirya cewar fitilar wasannin Olympic zata cigaba da ci a Lambun Tuileries dake gidan adana kayan tarihi na Louvre tsawon lokacin da za'a dauka ana gudanar da wasannin birnin Paris tsakanin watannin Yuli da Agusta masu zuwa
Dan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci kwallon farko da bugun fenariti a minti na 38. A minti na 84 ne kuma Ademola Lookman ya zura tasa kwallon.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa an ga tsohon dan wasan na Brazil mai shekaru 40 yana barin gidansa da ke Sao Paulo a cikin wata bakar motar ‘yan sanda.
Jose Peserio ya sanar da gama aikinsa na horar da 'yan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya bayan tawagar ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a kasar Ivory Coast.
A yau Alhamis, hukumar kwallon kafar kasar Saudiya ta dakatar da Christiano Ronaldo daga bugu wasa guda sakamakon wata alama daya nuna da yatsunsa a tsakiyar fili a makon daya gabata wacce aka hakikance cewar tsokana ce.
Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta bayyana cewar, kotun hukunta laifin shan kwayoyin kara kuzari tsakanin ‘yan wasa ta Italiya ta dakatar da tauraron dan wasan Faransa Paul Pogba daga harkar kwallon kafa tsawon shekaru 4 bayan an tabbatar cewa akwai sinadarin kara kuzari a cikin jininsa.
Kungiyar kwallon kafa ta Chippa United ta wallafa a shafinta na X cewar, Nwabali na daga cikin ‘yan wasan da suka yi fice a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023.
Lauyoyin matar da ta shigar da Alves kara sun ce sun gamsu da hukuncin da kotun ta Barcelona ta yanke.
A karon farko cikin shekaru 19 a gasar kwallon zari ruga ta NFL an samu kungiyar data sake maimaita nasara.
Domin Kari