Ministan Yadda Labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris ne ya bayana hakan a yau litinin da yake hira da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
Hakan a cewar NBS na nuni da cewa an samu karin kashi 0.24 idan aka kwatanta da wanda aka gani a watan Mayu wanda ya nuna kashi 33.45.
Zabubbukan zuwa ne bayan da Kotun Koli ta bada ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi, inda ta umarci gwamnatin tarayya ta biya kaso 20.60 cikin 100 na kason kudaden kananan hukumomin zuwa asusun ajiyarsu kai tsaye kuma ba cikin asusun ajiyar da gwamnoni ke juyawa ba.
A farkon watan Yuli Ministan noman Najeriya Abubakar Kyari ya ce gwamnatin tarayya za ta cire kudaden haraji wajen shiga da masara, alkama da wasu nau’ukan hatsi tsawon kwanaki 150.
Hatsarin da ya faru ranar Juma’a shi ne mafi muni da aka gani tun bayan wanda ya faru a watan Nuwamban 2021, a lokacin da wani katafaren gini ya ruguje a birnin Legas har akalla mutane 45 suka mutu.
A sanarwar da mai magana da yawun Shugaba Tinubun, Ajuri Ngelale ya fitar, yace “harin da aka kai wa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, abu ne mai kyama kuma ya wuce kololuwar ka'idojin dimokradiyya.
Hukumar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fafutukar tara isassun kudade don magance matsalar karancin abinci a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Jami’ai sun ce karuwar tashe tashen hankula a duniya sun sa kasashen da ke neman taimako gwagwarmayar nema wa kansu mafita.
Mai magana da yawun gwamnan, Suleiman Bala Idris, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a jiya Alhamis, inda yace majalisar tsaron jihar ta yanke shawarar takaita zirga-zirgar baburan ne a yayin wani taron gaggawa daya gudana a Larabar data gabata.
Saleh Mamman ya gurfana a gaban kotu ne a bisa tuhume-tuhume 12 dake da nasaba da hada baki domin halasta kudaden haram da mallaka tare da amfani da kudaden ta haramtacciyar hanya.
Majalisar Dokoki a Najeriya ta ce za ta daidaita duk wasu matakai na tabbatuwar cin gashin kan kananan hukumomi, yadda za su kaucewa tsangwamar gwamnonin jihohin kasar.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na rana a unguwar Busa Buji da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.
Domin Kari