Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada sababbin Sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Karaye, Rano da kuma Gaya.
Bayan shafe kwananki 20 a hannun yan bindiga, Hajiya Hauwa’u Adamu mahaifiyar mawakin Najeriya Dauda Kahutu Rarara da aka fi sani da Rarara ta samu kubuta da saduwa da ‘danta.
Yan Nigeria na ci gaba da maida martani akan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na raba tireloli ashirin -ashirin na kayan abinci ga kowacce jiha da ke fadin kasar,
Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta bayyana cewa, kayayyakin amfanin yau da kullum na cigaba da hauhawa a Najeriya babu ƙakkautawa inda farashin kayayyakin masarufi ya tashi da kaso 11.34 % idan aka kwatanta da farashinsa a shekarar da ta gabata.
Gwamana Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan kudirin dokar kafa masarautu ta bana da Majalisar Dokokin jihar ta zartar.
Babban likitan Alhazan Dokta Abubakar Adamu Isma’il ya yi bayanin alkaluman da aka tattara bayan kammala aikin hajjin na wadanda a ka rasa inda ya tabbatar cewa “jimilla gaba daya in ka hada da Madina da Makkah da Masha’ir mutum 15 kenan.
Gwamnatin Kano ta shigar da sabbin tuhume-tuhume akan tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyar apc na kasa mai ci, Dr. Abdullahi Ganduje.
Majalisar Dokokin Kano ta zartar da kudirin kafa masarautu a jihar na bana, domin kirkiro karin masarautu 3 masu daraja ta 2.
Alkaluman baya-bayan nan daga ofishin kididdiga na kasa sun nuna cewa hauhawar farashin ta zarta kaso 40 cikin 100 a ‘yan watannin baya, abinda ya sanya farashin kayan masarufi yafi karfin miliyoyin ‘yan Najeriya.
Wannan hukunci ya ci karo da wanda babbar kotun tarayya ta Kano ta zartar wacce ta soke rattaba hannu akan sabuwar dokar masarautu da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi inda ta ce dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II ya sabawa doka.
Domin Kari