Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Fara Shirin Kwaso mutanen da ke zama a kasar Lebanon, biyo bayan ta'azzarar rikici tsakanin Isra'ila da Iran.
Cikin daren Laraba, dakarun Isra’ilan sun kai wasu sabbin hare-haren sama a wata tungar mayakan Hezbollah da ke wajen kudancin birnin Beirut.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an tsinci gawarwakin mutum 16, mata biyu maza 14.
A sanarwar da kakakin jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar, tace jawabin shugaban ya nuna cewa babu fatan samun haske anan gaba “karkashin gwamnatin apc da bata san inda ta sa gaba ba kuma babu ruwanta da muradun ‘yan Najeriya”.
Bayo Onanuga, yace Tinubu zai yi amfani da makonni 2 ne a matsayin hutun dake hade da aiki domin sake nazarin sauye-sauyen gwamnatinsa akan tattalin arziki
A yau Laraba, Isra’ila ta ayyana cewa Sakatare Janar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ba nagartaccen mutum bane, inda ta zarge shi da gaza fitowa karara ya yi allawadai da harin makami mai linzamin da Iran ta kai mata.
Babban daraktan NSEMA, Alhaji Abdullahi Baba-Arah yace an samu nasarar ne sakamakon kai daukin gaggawa da al’umma ‘yan sa kai suka yi.
A cewar sanarwar da sakataren yada labaran karamar hukumar Mokwa, Abubakar Dakani ya fitar, kwale-kwalen na dauke ne da fiye fasinjoji 300 lokacin da ya kife a kogin Gbajibo da ya yi kwaurin suna a karamar hukumar ta jihar Neja.
Olukoyede ya yi wadannan kalaman ne a Abuja a ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2024, a cikin sakon bikin ranar ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya.
Hukumar Kula da Jini ta kasa ta Najeriya ta ce a shekarar 2023 kasar tana samun kusan kashi 27 cikin 100 na jinin da ake bukata, abin da masana suka ce ya gaza matuka.
Abokan takarar biyu sun amince cewa yawan 'yan gudun hijirar da ke cikin Amurka ba bisa ka’ida ba babbar matsala ce.
A yayin bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga al’ummar kasar inda ya yaba da irin gwagwarmayar da ‘yan Najeriya da dama suka fuskanta tare da bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ke yi na shawo kan wadannan kalubale ta hanyar kawo sauyi mai dorewa.
Domin Kari