A jiya Talata, jam’iyyar pdp ta bayyana cewar jawabin shugaban Najeriya Bola Tinubu na bikin samun ‘yancin kan Najeriya karo na 64 ya sake tabbatar da “halin ko in kula din gwamnatinsa game da wahalhalu da bukatun ‘yan Najeriya”.
“’Yan Najeriya sun yi mamakin yadda jawabin shugaban ya kasance bata lokaci kasancewar ya kasa warware matsaloli ko samarda mafita ga dimbin matsalolin tattalin arziki dana tsaro da gwamnatin apn din ta haddasa, wadanda ke illata ‘yan Najeriya,” a cewarsa.
Babbar jam’iyyar adawar ta kara da cewar jawabin shugaban kasar ya gaza amsa kiraye-kirayen milyoyin ‘yan Najeriya, sannan Tinubu ya ki ya sake nazarin manufofin gwamnatinsa masu wahalarwa.
Gazawar mai girma shugaban kasa ta jin koken ‘yan Najeriya ta hanyar sassauta farashin fetur da samar da guraben aikin yi da daga darajar Naira ta hanyar rage wadakar da gwamnatinsa ke yi tare da zuba kudaden kai tsaye wajen sake farfado da masana’antun da suka durkushe ya nuna karara cewar gwamnatin APC babu ruwanta da ‘yan Najeriya musammanma matasa.
Dandalin Mu Tattauna