Umarnin ministan na zuwa ne bayan rahoton da TCN ya fitar na cewar babban layin wutar ya sake katsewa da misalin karfe 11.29 na safiyar jiya Alhamis, 7 ga watan Nuwambar 2024, wacce karuwar da aka samu ta karfin lantarkin daga 50.33hz zuwa 51.44hz ya haddasa shi.
Gwamna Abba Yusuf ya bayyana kirarin da mara tushe, inda ya jaddada dadewa da kuma karfin dangantakarsa da Kwankwaso.
Yan Najeriya da wasu 'yan Ghana kimanin arba’in da hudu aka mayar kasashensu na asali bayan da aka samesu da laifin zama ba bisa ka’ida ba a Britaniya.
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da bullar sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ke gudanar da ayukkan ta a jihohin Sokoto da Kebbi, lamarin da ya sa masana lamurran tsaro jan hankalin mahukunta a kan daukar matakan hanzari kada wankin hula ya kai dare.
An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari na gwamnatin tarayyar Amurka bisa samunsa da hannu a wani gagarumin zamba ta yanar gizo da ya ci zarafin mutane sama da 400 a fadin Amurka wanda ya yi sanadin asarar kusan dala miliyan 20 baki daya.
Kamfanin wutar lantarki ya bayyana dalilin sake rugujewar tashar wutar lantarki ta kasa a karo na 12.
Binciken da aka gudanar akan shafin dake bada bayanai akan babban layin lantarkin na Najeriya (niggrid.org), ya nuna cewa da misalin karfe 11.30 na safiya yawan lantarkin dake kan babban layin ya sauka gaba daya al’amarin da ya shafi ilahirin kamfanonin dake samar da lantarkin a fadin kasar.
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bada makamancin wannan umarni a sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya fitar.
Sabon farashin mitocin zai fara aiki ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwambar da muke ciki, a cewar sakonnin da kamfanonin rarraba hasken lantarkin suka wallafa a shafukansu na sada zumunta.
An gudanar da gwajin lafiya ga masu zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagarin da aka sako din tare da basu shawarwari akan yadda zasu zamo mutane nagari da zasu amfani kansu dama al’umma baki daya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shiga sahum sauran Shugabannin duniya wajen taya Trump murnar sake zabensa a matsayin Shugaban kasar Amurka na 47.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ne ya fada cikin wata sanarwa da aka fitar cewa Janar Lagbaja dan shekaru 56, ya rasu ne ranar Talata a birnin Legas bayan fama da rashin lafiya
Domin Kari