Yayin mika rahoton, shugaban kwamitin Babajimi Benson, yace Laftanar Janar Oluyede ya cika dukkanin bukatu.
Yayin da yake jawabi ga gamayyar ‘yan dimokiradiyyar arewa karkashin jagorancin Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, Gowon yace yana takaici game da matsalar rashin tsaron Najeriya.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba a tsara kudurorin domin wani yanki ba sai dai don a bunkasa Najeriya baki daya.
Majalisar ta bukaci kwamitocinta a kan kudi da hakar danyen mai da cinikin albarkatun man fetur su binciki rahoton da hukumar rabon arzikin kasa dake zargin kamfanin man Najeriya (NNPCL) da rike Naira tiriliyan 8.48 a matsayin kudaden tallafin man fetur din da aka karba.
Ministan yace batun iskar hydrogen a Najeriya a bayyane yake, kasancewa Allah ya albarkaci kasar da dimbin albarkatun da za a iya sabuntawa, daga hasken rana dake yankin arewaci zuwa iskar dake yankunan gabar tekun dake kudu.
EFCC ta shigar tuhumar zargin aikata almundahanar Naira bilIyan 110 a kan tsohon gwamnan.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar ya dawo Abuja da yammacin yau Laraba.
Hukumomin Najeriya na neman hanyar kaddamar da babban Shirin kare cin zarafin jinsi, ko GBV a fadin kasar.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Yemi Cardoso ne ya sanar da hakan a Abuja a yau Talata yayin taron kwamitin manufofin kudin bankin na karshe a bana da ya gudana a shelkwatar babban bankin.
Domin Kari