Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ta fara shirye-shiryen yadda kasar za ta amfana da tsarin tattalin arzikin sinadarin iskar hydrogen na duniya da ake hasashen zai ci gaba da habaka zuwa fiye da dala biliyan 200 kan nan da shekarar 2030.
A jawabinsa yayin taron tattalin arzikin hydrogen na farko a Abuja a jiya Talata, karamin ministan albarkatun man fetur (bangaren iskar gas), Ekperikpe Ekpo yace iskar gas din da ake samarwa yayin amfani da makamashin da ake iya sabuntawa zai samarda wata dama ta musamman da zata cike gibin bukatar Najeriya ta makamashi.
A cewarsa, batun iskar hydrogen a Najeriya a bayyane yake, kasancewa Allah ya albarkaci kasar da dimbin albarkatun da za a iya sabuntawa, daga hasken rana dake yankin arewaci zuwa iskar dake yankunan gabar tekun dake kudu.
Ministan ya kara da cewar wurin da Allah ya ajiye Najeriya ya bata kyakkyawar damar cin kasuwannin nahiyoyin Turai da Afirka, inda yace za a iya yin amfani da bututun iskar gas din da ake da shi yanzu wajen yin safarar hydrogen din.
A nasa jawabin shima, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, wanda ya samu wakilcin hadimin shugaban kasa na musamman akan lantarki da kayayyakin more rayuwa, Sadiq Wanka, yace Najeriya zata juya akalarta ga iskar hydrogen wajen biyan bukatunta na makamashi, inda yace domin cimma wannan katafaren buri, yana da matukar muhimmanci a gina kwakkwaran layin samar da lantarki ta mabambantan makamashi.
Dandalin Mu Tattauna