Akalla mutum 10 suka rasa rayukansu, yayin da da dama suka jikkata a lokacin wani turmutsutsi da ya auku a Cocin Holy Trinity Catholic Church da ke yankin Maitama a Abuja a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da ake raba tallafin abinci a Mujami’ar.
Rundunar ‘yan sandar babban birnin na Najeriya wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin da adadin wadanda suka mutu, ta ce rayukan yara hudu sun salwanta.
“Sannan lamarin ya jikkata mutane takwas da suka samu raunuka daban-daban. Daga cikin wadanda suka jikkata an sallami mutum hudu bayan da aka ba su kulawa.” In ji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja SP Josphine Adeh.
Bayanai sun yi nuni da cewa an shirya rabon tallafin ne don a taimakawa marasa karfi yayin da aka tunkari bukukuwan Kirsimeti.
Wasu da suka shaida lamarin sun ce da misalin karfe 7 na safe aka samu turmutsutsin.
Dandalin Mu Tattauna