Alkaluma Jami’ar Johns Hopkins dake kididdigar masu dauke da cutar coronavirus na nuni da cewa Amurka ta zarra da adadin wadanda suka kamu da coronavirus mutum miliyan 9 a juma’ar nan, inda aka samu sababbin kamuwa miliyan 1 a cikin makonni biyu.
A jiya Litinin hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO ta sake yiwa kasashe kashedi cewa a daina saka siyasa a harkar annobar COVID-19, tana mai cewa yin haka na kawo rudani da rashin girmama masana kimiya kana cutar na kara ta’azzara.
Tattaunawa da Dr. Mustapha Ahmed Yusuf na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano akan sabuwar fasahar warkar da gyambo ko miki ko mummunan rauni cikin sauri wato "Maggot Therapy"
Hasashen da shugaban Amurka Donald Trump cewa za a samar da maganin rigakafin coronavirus kafin ranar uku ga watan Nuwamba da za a yi zabe ba zai cika ba.
LAFIYA UWAR JIKI:Tattaunawa da Likita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano Dr. Mustapha Ahmed Yusuf akan sabuwar fasahar warkar da miki ko gymbo, ko mummunan rauni cikin sauki. Tuni Asibitin na Malam Aminu Kano suka fara amfani da fasahar kuma kwalliya na bayan kudin sabulu, a cewar Dr. Mustafa.
Ma'aikatar lafiya ta jahar Filato da ke Arewacin Najeriya ta ce ta samo wata sabuwar dabarar yaki da cutar coronavirus a jihar.
Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya bada kayakin tallafi domin yaki da cutar COVID-19 ga gwamnatin jihar Bauchi.
Hukumar NCDC mai kula da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an samu karin mutum 120, da suka kamu da cutar COVID-19 a ranar Litinin, 05 ga watan Oktoba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da asubahin yau Jumma'a cewa shi da Uwargidansa Malania sun kama cutar Coronavirus
Wani tsohon ma'aikaci a kasar Birtaniya ya bayyana cewa bai taba rashin lafiya ba a rayuwarsa, kuma ya shafe shekaru saba'in bai ga likita ba,
Domin Kari