Masu bincike a jami’ar Copenhagen, da wadansu cibiyoyin bincike uku da suka hada da wurin bincike na Seattle, da jami’ar Oxford, da wani wurin bincike a Tanzania da kuma Kamfanin magunguna na Retrogenix LTD, sun gano yadda kwayoyin cutar zazzabin cizon sauro suke girma a cikin jini, su haddasa zazazabin cizon sauro mai zafi.