Ya zuwa farkon Agusta, yara 43 aka samu rahoton sun kamu da kwayar cutar Polio ta WPV, idan an kwatanta da yara 81 a shekarar da ta shige.
An gudanar da makon shayar da jarirai da nonon uwa a jihar Naija da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a cikin watan Agusta kowacce shekara.
Jami’ain aikin magani a Jamhuriyar Nijar sun ja hankalin al’umma game da matakan kare kansu daga kamuwa da zazzabin cizon sauro ganin ana kara shiga damina.
Rahoton wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, kimanin mutane dubu casa’in da biyar suke mutuwa kowacce rana a shekara saboda da shakar hayakin murhu.
Wata kungiya mai suna TSHIP, dake aiki tare da hukumar raya kasashen Africa, USAID, ta bayanna cewa an sami wani magani mai hana mata zubar da jini bayan haihuwa.
Binciken ya nuna cewa, kimanin kashi 52% na kananan yara tsakanin watanni shida zuwa biyar na haihuwa ya nuna cewa, suna dauke da kwayar cutar zazzabin cizon sauro
Likitoci sun yi jan hankali ga mutanen da suke fama da cututuka kamar ciown suga da hawan jinni da kuma kyambon ciki a kan abincin da zasu rika ci domin kawo rigakafi ga cututukan da suke fama da su.
Taron shugbannin nahiyar Afrika ya bukaci kowacce kasa a Afrika ta kashe kashi goma sha biyar cikin dari na kasafin kudinta domin dakile nau’in wadannan cututukan
Kungiyar WRAPA ta yaba yadda kungiyoyi da malamai suka tashi tsaye haikan wajen wayar da kan al’umma a kan muhimmancin tazarar haihuwa
Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako na Jihar Sokoto yace yanzu watanni 8 ke nan ba a samu bullar cutar ko sau daya ba a jihar
Masana masu bincike sun gano wata sabuwar hanya ta gano mutane masu dauke da tarin fuka, ko TB, ta hanyar gano wasu nau’oin Protein dake bin jiki idan huhun mutum ya fara lalacewa.
Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin kashi hamsin bisa dari na mata masu ciki a Nigeriya da sauran kasashe na Saharan Africa basu zuwa awo a kalla sau hudu, yawan ziyarar da Majalisar Lafiya duniya ta bada shawara, domin tabbatar da lafiyar iyaye mata da jariransu.
Domin Kari